Manyan mutanen da suka taimakawa Janar Sani Abacha ya saci Dala miliyan 23 a kasar waje

Manyan mutanen da suka taimakawa Janar Sani Abacha ya saci Dala miliyan 23 a kasar waje

  • Hukumomin kasar Birtaniya sun gano wasu makudan Dalolin da ake zargin Sani Abacha ya sata
  • Binciken da aka yi ya nuna kamfanin Mecosta Securities Inc ya saci sama da Dala miliyan 20 a Turai
  • ‘Ya ‘yan Janar Sani Abacha da wani na-kusa da dangin sun taka rawar gani wajen wannan badakala

Kwanan nan hukumar National Crime Agency (NCA) mai binciken laifuffuka a kasar Ingila ta gano wata badakala da dangin Sani Abacha suka tafka.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Alhaji Mohammed Sani Abacha ya hakura da wani kamfaninsu mai suna Mecosta Securities Inc a Birtaniya.

Binciken da aka yi ya nuna cewa wannan kamfanin tsaro na Mecosta Securities yana da akawun a wani bankin Landan, inda a nan ne aka bankado kudin sata.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

A Oktoban 1995 aka bude akawun a wannan banki a Ingila domin a ajiye dukiyar kamfanin. Daga baya, an gano an rika amfani da asusun wajen satar miliyoyi.

Wanda yake kula da asusun bankin kamfanin shi ne Sanata Atiku Abubakar Bagudu. A halin yanzu gwamna ne a jihar Kebbi kuma babba a jam’iyyar APC.

Atiku Abubakar Bagudu

Jaridar ta ce a cikin wadanda suke kula da kadarori da dukiyar da Sani Abacha da iyalinsa suka sata, takardu sun nuna babu kamar Gwamna Atiku Abubakar Bagudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Binciken da hukumomi irinsu Transparency International suka yi ya nuna iyalin Abacha da na-kusa da shi sun saci kusan Dala biliyan biyar tsakanin 1993 da 1998.

Gwamnan Kebbi
Gwamnan Kebbi, Sanata Atiku Bagudu Hoto: @kbstgovt
Asali: Facebook

Daga shekarar 1998 zuwa yau, an gano $3.6bn da aka boye a ketare, wanda Bagudu yana da hannu.

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

Mohammed Abacha

Sabon binciken da aka yi ya nuna kamfanin Mecosta ya boye Dala miliyan 21.7 a babban bankin nan na Standard Bank da ke kasar Ingila da sunan Mohammed Abacha.

Haka zalika wannan kamfani yana da akalla dala miliyan 1.6 da ake zargin kudin sata ne da aka ajiye a HSBC. An yi wannan ne ta karkasin ‘dan tsohon shugaban kasar.

Alhaji Mohammed Abacha 'dan siyasa ne wanda ya taba neman takarar gwamna a jihar Kano.

Kafin a buga wannan rahoto, jaridar ta nemi jin ta bakin Gwamnan na jihar Kebbi, amma bai yarda ya ce komai ba. Shi ma Mohammed Abacha bai amsa wayarsa ba.

Badakalar rijiyar Malabu

Kwanaki aka ji labari Mohammed Abacha yace ya yi amfani da sunan Mohammed Sani wajen samun rijiyar OPL 245. Abacha ya bayyana haka da aka shari’a da shi a kotu.

‘Dan siyasar yace an cire sunansa daga kamfanin Malabu Oil and Gas a lokacin da yake gidan yari. Da farko Janar Sani Abacha ne yake da 30% na hannun jari a rijiyar man.

Asali: Legit.ng

Online view pixel